Duration 18:3

Tarihin Janar Murtala Muhammad: Shugaban Najeriya 4

5 592 watched
0
68
Published 18 Jul 2023

Janar Murtala Ramat Muhammad, sojan nan da hotonsa ke jikin N20 shi ne shugaban ƙasar Najeriya na huɗu bayan samun ƴancin kai. Watanninsa shida kacal a kan mulki amma ayyukan da ya yi sun sa ba za a taɓa mantawa da shi a tarihi ba. Shi ne ya jagoranci mayar da dimokradiyyar Najeriya tsarin shugaba mai cikakken iko irin na Amurka saɓanin tsarin firaminista irin na Burtaniya. Shi ya ƙirƙira ƙarin jihohi shida inda ya mayar da su daga 12 zuwa 19. Shi ne kuma ya zaɓi Abuja ta zama sabon Birnin Tarayyar Najeriya domin kaucewa matsalolin da ake fama da su a Legas. Ga shi kuma ya yi aiki babu sani babu sabo, ba kasala ba jan ƙafa wurin yaƙi da cin hanci da rashawa. Ya binciki ministoci da gwamnoni na gwamnatin da ya gada kuma ya ƙwato kadarorin da suka sata. Ya kuma sallami dubunnan ma’aikata da ya samu da laifi ko ya fahimci ba a buƙatarsu. Sai dai ana ganin wannan matakin shi ne ya tashi hankalin waɗanda suka rage suka shiga tafka rashawa don shirin ko-ta-kwana. A ɓangaren ƙasashen ƙetare ya lakace hahncin Turawan Yamma inda ya soki yadda suke katsalandan cikin harkokin Afirka. Har yanzu akwai waɗanda suke ganin da haɗin bakin Amurka aka shirya masa juyin mulki saboda ya kawo mata cikas wurin cimma manufofinta. Bayan da aka kashe shi a juyin mulkin da bai yi nasara ba, ƴan Najeriya sun shiga jimami da matsanancin alhini. Kuma domin tunawa da shi a ka sanyawa babbar tashar jiragen sama dake Legas sunansa kuma aka ƙirƙiro Naira Ashirin domin karrama shi.

Category

Show more

Comments - 16